Isa ga babban shafi
Algeria

Hukumar zaben Algeria ta takaita adadin 'yan takarar shugaban kasa

Hukumar zaben Algeria, ta ce ‘yan takara 5 ne kawai za su fafata a zaben shugabancin kasar da zai gudana rana 12 ga watan Disamba, zaben da ake fatan zai kawo karshen rikicin siyasar da har yanzu kasar ke fuskanta, duk da murabus din tsohon shugaba Abdel Aziz Bouteflika cikin watan Afrilu.

Masu zanga-zangar adawa da zaben shugaban kasa a Algiers, babban birnin Algeria. 1/10/2019.
Masu zanga-zangar adawa da zaben shugaban kasa a Algiers, babban birnin Algeria. 1/10/2019. REUTERS/Ramzi Boudina
Talla

Daga cikin ‘yan takarar biyar akwai tsaffin Fira Ministan kasar ta Algeria 2, AbdulMajid Tebboune da Ali Benflis.

Sai dai yan adawa sun yi watsi da matakin takaita yawan ‘yan takarar zuwa 5, la’akari dacewa mutane 23 suka mika takardun neman amincewa a basu damar tsayawa, amma hukumar zaben Algerian ta soke bukatun nasu, saboda gaza cika wasu ka’idoji.

A halin da ake ciki kuma har yanzu dubban ‘yan kasar ne ke gudanar da zanga-zanga a kowane mako, don adawa da gudanar zaben, gami da zargin cewa, ko da ya gudanan, ba za a yi adalci ba, ganin cewar har yanzu akwai sauran mukarraban shugaba Bouteflika mai murabus da ke cikin gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.