Kano ke kan gaba wajen fama da gurbacewar Iska a Afrika - Masana
Wani rahoto da wata cibiya a kasar Switzerland mai suna IQAIR Airvisual ta fitar, ya sanya birnin Kano na arewacin Najeriya kan gaba a cikin biranen dake fama da matsalar gurbatacciyar iska a nahiyar Afrika.Rahoton wanda cibiyar dake bibiyar ingancin muhalli a duniya ta fitar, yace birnin Kamfala na Uganda ne ke biye da Kano a baya, sai kuma Addis Ababa na Habasha dake matsayi na uku.Daga Kanon wakilinmu Abubakar Abdulkadir DanGambo ya hada mana rahoto kan batun gubacewar iskar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kano ke kan gaba a fama da gurbacewar Iska a Afrika - Masana
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu