Isa ga babban shafi

Eto'o ya dauki alhakin tura Iya a kurkuku

Tsohon kaftin din kungiyar kwalon kafar kasar Kamaru Indomitable Lions, Samuel Eto'o Fils, ya nuna damuwa kan ci gaba da tsare tsohon shugaban hukumar kwalon kafar kasar Iya Mohammed, inda ya roki shugaban kasa Paul Biya da yayi wa Allah ya sake shi.

Samuel Eto'o da shugaban hukumar CAF Ahmad Ahmad a kasar Liberia a shekarar 2018.
Samuel Eto'o da shugaban hukumar CAF Ahmad Ahmad a kasar Liberia a shekarar 2018. ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Cikin wata hira da aka watsa kai tsaye a wasu gidajen radio 4 na kasar Kamaru a ranar Alhamis ne, Samuel Eto'o wanda bai nuna nadamar kokarin da ya yi a lokacin da yake Kaftin din tawagar, tsakanin shekarun 2011 zuwa 2013, wajen ganin Iya Mohammed ya bar jagorancin kungiyar kwalon kafar kasar ba.

A watan Yuni shekarar 2013, ne mahukuntan Kamaru suka garkeme Iya Mohammed a kurkun kwandengi, bayan dawowarsa daga rakiyar ‘yan wasan kasar daga kasar Togo, kuma tun daga wancan lokaci aka ci gaba da tsare shi, bisa zargin albazaranci da kudin Kamafanin audugar kasar Sodecoton da can ma yake jagoranta.

Kuma tun bayan tsare shi, makusantar Iya, ke zargin Samuel Eto'o da shirya makarkashiya domin cire shi daga shugabancin kungiyar, ganin fada-aji da Eto ke da shi a gwamnatin kasar, da kuma rashin dasawarsu da iya.

Yanzu dai ta tabbata ta kare, Samuel Eto'o ya tabbatar da wannan zargi kai tsaye a kafafen radion, dangene da bita da kullin da ya yiwa dan asalin yankin arewacin kasar, kuma tsohon shugaban kungiyar kwallon kafar kasar, kuma shugaban kamfanin audugar kasar, kana mamallakin kungiyar kwallon kafar jihar sa Garoua, wato Coton Sports da tayi suna a kasashen Afrika dama duniya, da yanzu haka ya kwashe shekaru 6 a kurku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.