Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotun Koli ta bayyana dalillan korar karar Atiku

Kotun Kolin Najeriya yau juma’a ta bayyana dalilan da suka sa tayi watsi da karar da dan takarar Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da Jam’iyyar sa suka shigar, inda suke kalubalantar zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari a farkon wannan shekara.

Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben shugabancin Najeriya Atiku Abubakar.
Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben shugabancin Najeriya Atiku Abubakar. REUTERS/Nyancho NwaNri
Talla

Kotun tace Jam’iyyar PDP ta gaza gabatar da shaidun da tace tana da su 250,000 a kotun dake sauraron kararrakin zabe domin tabbatar da zargin da take yi.

Kotun ta kuma ce ‘dan takarar Jam’iyyar APC Buhari yana da cikakken halarcin tsayawa takarar zaben da akayi, yayin da PDP ta gaza gabatar da shaidar dake adawa da haka.

Kotun ta bayyana batutuwa biyu da suka mamaye karar Jam’iyyar PDP da ‘dan takarar ta Atiku Abubakar da suka hada da rashin amfani da dokar zabe da kuma rashin cika sharadodin tsayawa takarar shugaban kasa Buhari.

Alkalin kotun John Okoro ya ce dangane da rashin amfani da dokar zabe, ya zama wajibi Jam’iyyar PDP ta gabatar da gamsassun shaidu domin tabbatar da sahihancin korafin su amma bata yi haka ba, yayin da ta kasa gabatar da shaida akai wadanda suka ganin da idan su yadda aka saba ka’ida.

Dangane da cika sharuddan tsayawa takarar zabe kuwa, alkalin yace Magana ce ta dokar kasa wadda tace dole ne dan takarar yayi karatu zuwa matakin sakandare ko makamancin haka, kamar yadda sashe na 318 ya bayyana, kuma dan takarar APC Muhammadu Buhari ya cika wannan sharadi.

Kotun tace wadanna dalilai suka sa kotun koli tayi watsi da karar da kuma tababtar da zaben Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.