rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Ta'addanci Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An samu raguwar rasa rayuka

media
Wani harin ta'addanci AAP/James Ross/via REUTERS

Cibiyar dake sanya ido kan harin ta’addancin da ake samu a Duniya tace an samu raguwar mace macen da ake samu sakamakon harharin da ya kai sama da kashi 15 a shekarar 2018, duk da samu karuwar kasashen dake fuskantar irin wannan tashin hankalin a cikin wannan shekara ta 2019.


Rahotan yace sabanin adadin mutane 33,555 da aka kashe a shekarar 2014, lokacin da mayakan IS suka yaudari dubban mutane zuwa jihadi a Gabas ta Tsakiya, adadin ya ragu zuwa 15,952 a shekarar 2018.

Rahotan yace kasar da aka fi samun raguwar mace macen a shekarar 2018 itace Iraqi wadda ta bayyana samun nasara kan mayakan IS a shekarar 2017, sai kuma Somalia inda dakarun Amurka ke cigaba da kai hare hare.

Kasar Afghanistan inda Taliban ta maye gurbin IS a matsayin kungiyar Yan ta’adda mafi girma ke kan gaba wajen kai hare hare 1,443, inda aka kashe mutane 7,379, sai Iraqi mai hare hare 1,131 wanda ya hallaka mutane 1,054 sai kuma Najeriya a matsayi na 3 sakamakon hare haren boko haram 562 wanda ya kashe mutane 2,040.

Rahotan yace Syria ke matsayi na 4 da hare hare 131 wanda yayi sanadiyar asarar rayuka 662, yayin da a nahiyar Turai inda babu wani babban harin ta’addanci da akai a shekarar 2018, adadin mutanen da aka kashe ya ragu daga 200 a shekarar 2017 zuwa 62.