Isa ga babban shafi
Najeriya

An kori Sarkin Bai saboda yin mubaya’a ga Sarkin Kano

Rahotanni daga birnin Kano dake Najeriya sun ce Sarkin Bichi, Aminu Ado Bayero ya kori Hakimin Dambatta kuma daya daga cikin masu zaben Sarkin Kano, wato Mukhtar Adnan daga kujerar ta hakimci.

An rage karfin masarautar Kano da karin masarautu
An rage karfin masarautar Kano da karin masarautu Dr.Meddy
Talla

An dai nada Adnan a matsayin Hakimin Dambatta kuma Sarkin Bai na Kano ne a shekarar 1954, kuma yana daga cikin wadanda suka zabi Sarkin Kano Ado Bayero shekaru 9 bayan nadin da aka masa.

Rahotanni sun ce korar Sarkin Bai mai shekaru 93 a duniya nada nasaba da biyayyar da yake yiwa Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu da kuma adawar sa da kirkiro sabbin masarautu a Jihar ta Kano.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da sabuwar Masarautar Karaye ta kori Hakimin Kiru, Ibrahim Hamza da kuma Hakimin Rimin Gado, Shehu Muhammad daga mukaman su.

Mai Magana da yawun Masarautar Karaye Haruna Gundumawa yace Masarautar ta sanar da nada Auwal Muhammad a matsayin sabon Hakimin Rimin Gado, Magajin Rafin Karaye, yayin da aka nada Alhaji Garba Alhaji a matsayin Hakimin Kiru kuma Danmadamin Karaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.