Isa ga babban shafi
DR Congo-Ebola

An samu koma baya a yaki da Ebola- WHO

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce a karon farko, an fuskanci koma baya a yakin da ake da cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, inda wani mara lafiya da ya warke daga cutar, ya sake kamuwa da ita.

Jami'an WHO a sansanin kula da masu fama da cutar Ebola da ke Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo.
Jami'an WHO a sansanin kula da masu fama da cutar Ebola da ke Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo. REUTERS/Baz Ratner/File Photo
Talla

Hukumar ta WHO ta ce lamarin ya faru ne a arewacin lardin Kivu.

Tun bayan sake bullar da Ebolan ta yi a Jamhuriyar Congo cikin shekarar da ta gabata, cutar ta hallaka sama da mutane dubu 2 da 200, yayinda wasu sama da dubu 3 da 300 suka kamu da ita.

Ko a baya-bayan nan akwai bayanai da ke nuna yadda bangaren lafiyar na Jamhuriyyar Demokradiyyar Demokradiyyar Congo ya yi almubazzaranci da kudaden yaki da cutar ta Ebola.

Haka zalika an fuskancin karancin rarraba magungunan yaki da cutar ta Ebola a sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.