Isa ga babban shafi
Libya-Turkiya

Libya ta nemi taimakon Turkiya ta bangaren Soji

Gwamnatin hadin kan kasar Libya ta nemi taimakon Turkiya ta bangaren soji, taimakon da mai magana da sunan Shugaban kasar ta Turkiya ya tabbatar da cewa Turkiya zata bayar da amsa a kai.

Shugaban Turkiya, Recep Erdogan yayin ganawar sa da Firaministan Libya
Shugaban Turkiya, Recep Erdogan yayin ganawar sa da Firaministan Libya © Presidential Press Office/Handout via REUTERS
Talla

Ranaku 8 da 9 ga watan janairu shekarar 2020 mai kamawa ne majalisar kasar Turkiya za ta yi zaman ta na musaman domin duba irin rawar da Turkiya zata iya takawa dangane da bukatar hukumomin Tripoli.

A daya wajen hukumomin Rasha sun musanta labarin da ake ci gaba da yadawa na cewa Rasha ta tura da sojojin ta domin dafawa dakarun Janar Haftar dake yakar sojojin Tripoli.

Ranar 27 ga watan Nuwamba ne gwamnatin Ankara ta cimma yarjejeniya da gwamnatin hadin kan Libya dangane da batun dafa mata tareda aiko da sojojin a wannan yaki da ta ke yi da dakarun Janar Haftar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.