Isa ga babban shafi
Najeriya

JAMB ta janye bukatar katin dan kasa a jarabawar bana

A Najeriya hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu da ake kira JAMB ta janye kudirin hana duk wani dalibi da ba shi da lambar katin shaidar dan kasa ta NIN sukunin sayen fom din za na jarabawar don neman gurbi a manyan makarantun kasar.

Farfesa Ishaq Oloyede shugaban hukumar shirya jarabawar neman gurbi a manyan makarantu ta Najeriya JAMB.
Farfesa Ishaq Oloyede shugaban hukumar shirya jarabawar neman gurbi a manyan makarantu ta Najeriya JAMB. JAMB
Talla

Shugaban hukumar Farfesa Ishaq Oloyede, da ke tabbatar da hakan ga manema labarai a Abuja babban birnin Najeriyar, ya ce a wanna karon hukumar za ta daga kafa don bai wa dalibai damar mallakar katin shaidar dan kasar kafin badi.

Acewar Oloyede matakin na da nasaba da tangardar na’urar da hukumar samar da katin dan kasar ta samu da ya hana gudanar da aikin cikin hanzari.

Sai dai shugaban na hukumar JAMB ya ce rijistar jarabawar ta JAMB a shekara mai zuwa ta 2021 zai zama dole sai da bayanan katin dan kasar ga kowanne dalibi da ke Najeriyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.