Isa ga babban shafi
Afrika

An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta na wucin gadi a Libya

Gwamnatin Libya mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya ta amince da shirin tsagaita wuta,kiran da kasashen Rasha da Turkiyya suka aike ga janar Haftar da Fayyez Al Sarraj.

Kasashen Duniya na tattaunawa dangane da rikicin Libya
Kasashen Duniya na tattaunawa dangane da rikicin Libya Francisco Seco / POOL / AFP
Talla

Shugaban gwamnatin ta Libya, Fayez al-Sarraj ya ce yana maraba da duk wani shirin samar da zaman lafiya a kasar, amma bisa sharadin dole Haftar ya janye jiki daga yankunan da ya kame yana farmakar dakarun gwamnati.

A cewar Sarraj, Haftar ba shi da nufin ja da baya a yakin da ya faro,

Turai da kasashen Arewacin Afrika sun kaddamar da wani shirin sulhunta bangarorin ta fuskar diflomasiyya wajen ganin yaki bai sake barkewa a kasar ba, tare da neman bangarori biyu masu rikici da juna su sasanta.

Wannan mataki da aka cimma zai taimaka wajen sassanta bangarori na dan karamin lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.