Isa ga babban shafi
Afrika

Adadin dakarun Nijar da suka mutu a harin Shinagodar ya karu

Hukumomin tsaron Jamhuriyar Nijar, sun ce adadin sojojin kasar da ‘yan ta’adda suka halaka yayin farmakin da suka kai musu a ranar alhamis ya karu zuwa 89.

Sojojin Nijar da suka mutu a harin Inates
Sojojin Nijar da suka mutu a harin Inates RFI/Moussa Kaka
Talla

A ranar alhamis din da ta gabata, gwamnatin kasar ta ce dakarunra 25 ne suka kwanta dama yayin farmakin da ‘yan ta’addan suka kaiwa sansaninsu, a garin Chinagodrar, harin da daga bisani sojojin suka murkushe shi, tareda halaka maharan 63.

Harin makon na jiya dai a yanzu shi ne mafi muni da Nijar ta gani, bayan na watan da ya gabata, inda maharan suka halaka sojojin kasar 71.

Har yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai mummunan harin, sai dai Ministan tsaron Nijar Issoufu Katambe ya sha alwashin sojin kasar za su kaddamar da farmaki kan ‘yan ta’addan.

Wata kididdiga da cibiya mai zaman kanta, dake sa idanu da tattara alakalumma kan tashe-tashen hankula wato “Armed Conflict Location & Event Data Project, ta nuna cewar, hare-haren ta’addanci sun ninka sau akalla 4 a Jamhuriyar Nijar cikin shekara 1, inda kusan mutane 400 suka halaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.