Isa ga babban shafi
Amurka-Afrika

Amurka za ta rage yawan sojinta da ke nahiyar Afrika

Kasar Amurka ta sanar da aniyar rage dakarun Sojinta da ke yaki a Nahiyar Afrika, dai dai lokacin da rundunar tsaro ta NATO ke shirin karfafa dakarunta a yankin gabas ta tsakiya wanda ke da alaka da rikicin Amurkan da Iran da ke kara kazanta.

Shugaban Amurka Donald Trump a tsakiyar dakarun kasar da ke ketare.
Shugaban Amurka Donald Trump a tsakiyar dakarun kasar da ke ketare. Reuters/路透社
Talla

Cikin sanarwar da babban kwamandan rundunonin Sojin Amurka Janar Mark Milley, ya fitar ya bayyana cewa maimakon Afrika, kasar za ta yawaita dakarunta da ke yankin Amurkan da kuma Pacific don kalubalantar barazanar tsaron da su ke fuskanta.

Akalla Sojin Amurka dubu 7 ne ke cikin rundunonin yaki daban-daban a nahiyar Afrika ko da dai galibinsu na kasar Somalia inda su ke yaki da ta'addancin kungiyar Al- Shebaab.

Haka zalika, Amurkan na da Soji akalla dubu 2 da ke aikin bada horon Soji a kasashen Afrika 40 ciki har da wadanda ke tallafawa Sojin Faransa a rundunar tsaro ta Barkhane da ke yaki da ta'addanci a kasashen yankin Sahel.

Bugu da kari a kwanakin baya-bayan nan ne, shugaban Amurka Donald Trump ya nuna bukatar Wannan sanarwar Amurka na zuwa ne, biyo bayan kiran da shugaban kasar Donald Trump ya yi ga kungiyar Tsaro ta NATO da ta karfafa azama a Gabas ta Tsakiya.

Amurkan dai nada sansanin kuramen jirage a birnin Agadez na Jamhuriyar Nijar da ke ayyukan leken asiri a yankin Sahel, wanda aka kiyasata kasar ta kashe kimanin dala miliyan 100 akai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.