Isa ga babban shafi
Kamaru

'Kuri'ar raba gardama ce za ta magance rikicin Kamaru'

Kungiyar Lauyoyin Afrika ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta yi amfani da kuri’ar raba gardama domin kawo karshen zubar da jini a yankin da ake amfani da turancin Inglishi na Kasar Kamaru.

Masu zanga-zangar adawa d gwmnatin Kamaru rike da tutocin ambazonia.
Masu zanga-zangar adawa d gwmnatin Kamaru rike da tutocin ambazonia. REUTERS/via Reuters TV
Talla

A cikin wata wasika da ya aike wa Firaministan Birtaniya Boris Johnson, shugaban Kungiyar Lauyoyin Afrika Hannibal Uwaifo, ya ce kokarin kawo karshen tashe-tashen hankula a yankin ta hanyar amfani da  karfi, ba zai haifar da komai ba illa kara rincabewar al'amura.

A maimakon hakan kungiyar ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta yi amfani da kuri’ar jin ra’ayin jama’a a yankunan arewa maso yamma da kudu maso yammacin Kamaru domin bai wa al'umma daman zaben makomarsu da kansu.

A cikin wasikar ta ranar Juma’a 10 ga watan Janairu, Uwaifo ya ce nuna halin ko-in- kula daga bangaren Majalisar Dinkin Duniya da kuma yadda kasashe masu fada aji suka yi gum, sun taimaka wajen tsanantar halin da mutane ke ciki a yankin.

Yankunan arewa maso yamma da kudu maso yammacin kasar, na fafutukar ballewa  domin kafa Jamhuriyar Ambazonia, abin da ya haifar da rikici tare da rasa dumbin rayuka, yayin da dubbai suka guje wa gidajensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.