Maharba sun sake farmakar Fulani a Mali
Majalisar Dinkin Duniya ta koka da yadda hare-hare kan kauyuka a Mali ke ci gaba da ta’azzara dai dai lokacin da harin daren Alhamis din nan kan kauyukan Fulani ya hallaka mutane 14 tare da jikkata wasu mutum 2.
Wallafawa ranar:
Adadin na Majalisar Dinkin Duniya kan mutane da suka mutu a harin dai ya banbanta da adadin da jami’an tsaron kasar suka bayar da ya nuna mutane 15 suka kwanta dama a harin kabilancin.
A cewar ma’aikatar tsaron Mali dai, wasu mahaya ne kan babaura sanye da shiga irinta Maharba da aka fi sani da Dozo suka farmaki kauyen Siba tare da hallaka Fulanin.
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa baya ga mutanen 15 da suka mutu maza 5 mace guda, maharani sun kuma kone kauyen kurmus.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu