Isa ga babban shafi
Najeriya

Abdullahi Ganduje zai yi nadama lokacin da zai kawo karshen mulkin sa

Tsohon Gwamnan Jihar Kano dake Najeriya, Rabiu Musa Kwankwaso yace Gwamna mai ci Abdullahi Ganduje da mukarraban sa za suyi nadama lokacin da suka kawo karshen mulkin Jihar.

Dr Abdullahi Umar Ganduje gwamnan Kano
Dr Abdullahi Umar Ganduje gwamnan Kano kanostate.gov.ng
Talla

Yayin da yake jawabi a kafofin yada labaran Kano suka yada kai tsaye, Kwankwaso yayi zargin cewar Gwamnatin Ganduje banda yaudara da karya babu abinda take shukawa mutanen Kano.

Kwankwaso yace a karshen mulkin Ganduje zai ce yayi nadama, da ya mikawa wanda ya lashe zaben da akayi a shekarar 2019.

Wadannan kalamai na Kwankwaso kamar mayar da martani ne ga kalaman Gwamna Abdullahi Ganduje wanda ya bayyana shi a matsayin wanda ke kokarin sauya sheka zuwa APC domin takarar zaben shugaban kasa a shekarar 2023.

Yayin da yake karbar tsohon shugaban PDP Dr Rabi’u Usman Bichi da ya sauya sheka zuwa APC, Gwamna Ganduje ya bayyana Kwankwaso a matsayin mai tsananin son kan sa da kuma kin yabawa da rawar da wasu ke takawa.

Ganduje yace yafi kowa sanin wanene Kwankwaso da kuma dabarun siyasar sa tare da kuma yadda yake zama da jama’a kana da kin yabawa wadanda suka bada gudumawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.