Isa ga babban shafi
Afrika

Biliyoyin Farin dango sun afkawa gonaki a gabashin Afrika

Masana sun yi gargadin cewar, biliyoyin farin dangon dake afkawa gonaki da rumbunan abinci a sassan gabashin nahiyar Afrika, na da nasaba da sauyin yanayi na zafi ko sanyi, zalika barnar farin dangon ka iya sake munana halin farin da wasu sassan gabashin Afrikan ke ciki, la’akari da cewar basu gama farfadowa daga masifun na fari da ambaliyar da suka fuskanta ba.

Wani mazaunin kauyen Lemasulani dake lardin Samburu a Kenya, yayin kokarin korar Farin dangon da suka afkawa gonakinsu. 17/01/2020.
Wani mazaunin kauyen Lemasulani dake lardin Samburu a Kenya, yayin kokarin korar Farin dangon da suka afkawa gonakinsu. 17/01/2020. Njeri Mwangii / Reuters
Talla

A makon nan ne dai hukumar bunkasa noma da samar da abinci ta majalisar dinkin duniya FAO ta ce hadarin farin dangon da ya taso daga Habasha da Somalia zuwa Kenya, ya kai girman murabba’in kilomita dubu 2 da 400, kwatankwacin girman birnin Moscow, abinda ke nufin adadin farin zai iya kaiwa biliyan 200.

Hukumar ta FAO ta bayyana mamayar farin dangon a matsayin mafi muni da kasashen Habasha da Somalia suka gani cikin shekaru 25, mafi muni kuma cikin shekaru 70 a kasar Kenya.

Hukumar ta kuma yi gargadin cewar, muddin ba a dauki mataki ba, yawan farin dangon ka iya ninkawa sau 500 nan da zuwa watan Yuni, kuma farin za su bazu zuwa kasashen Uganda da Sudan, abinda zai kai ga tafka hasarar dimbin kayan abinci da sauran amfanin gona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.