Isa ga babban shafi

Kotun kolin Malawi ta soke zaben da ya baiwa shugaba maici nasara

Babbar Kotun kasar Malawi ta soke zaben shugaban kasar da akayi a watan Mayu wanda aka bayyana shugaba Peter Mutharika a matsayin wanda ya lashe domin yin wa’adi na biyu.

Lauyoyin Malawi lokacin korafi kan sakamkon zaben da ya baiwa shugaba mai ci nasara
Lauyoyin Malawi lokacin korafi kan sakamkon zaben da ya baiwa shugaba mai ci nasara MalawiTimes
Talla

Alkalin kotun Healey Potani yace sakamakon korafin da aka gabatar musu da kuma nazari da suka yi akai, sun gano cewar shugaba Mutharika bai samu nasarar zaben da akayi ranar 21 ga watan Mayu ba, saboda haka sun soke zaben, kuma sun bada umurnin gudanar da wani sabo nan da kwanaki 150 masu zuwa.

Ana fargabar cewar hukunci na iya haifar da tashin hankali tsakanin masu goyan bayan shugaba Mutharika da masu adawa da shi, wadanda suka yi ta zanga zanga tun bayan sanar da sakamakon zaben.

Rahotanni sun ce kafin zaman kotun na yau, motocin soji ne suka yiwa alkalan rakiya zuwa kotu, yayin da jirgin saman soji yayi ta shawagi lokacin da ake bada hukuncin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.