Isa ga babban shafi
Afrika

Guterres ya bayyana goyan baya don sassanta rikicin Libya daga AU

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana goyan bayan kungiyar kasashen Afirka ta AU wajen jagorancin sassanta rikicin kasar Libya, bayan ya amince da watsi da kungiyar da kasashen duniya suka yi wajen sasanta rikicin.

Zauren taron kungiyar kasashen Afrika na AU a Addis Abaaba
Zauren taron kungiyar kasashen Afrika na AU a Addis Abaaba RFI/Paulina Zidi
Talla

Guterres dake halartar taron kungiyar kasashen Afirka dake gudana a Addis Ababa yace ya fahimci fushin kungiyar, kuma ya zama wajibi a sanya ta cikin duk wani yunkuri.

Shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa da zai karbi shugabancin kungiyar AU daga ranar litinin yace shugabancin sa zai mayar da hankali kan warware rikicin kasar Libya.

Shugabannin kungiyar kasashen Afirka sun koka kan yadda aka sanya su a gefe, a yunkurin da kasashen Duniya keyi wajen sassanta bangarorin dake rikici a Libya, cikin su harda Majalisar Dinkin Duniya da wasu kasashen Turai.

Kasar Libya ta fada cikin tashin hankali tun daga shekarar 2011 lokacin da kungiyar NATO ta goyi bayan boren da ya kawar da shugaba Muammar Ghadafi daga karagar mulki.

Yanzu haka kasar a rabe take tsakanin gwamnatin dake samun goyan bayan Majalisar Dinkin Duniya da shugaban Yan Tawaye Janar Khalifa Haftar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.