Isa ga babban shafi
Mali

Sojin Faransa sun halaka 'yan ta'adda 30 a Mali

Rundunar sojin Faransa, ta ce dakarunta sun yi nasarar halaka mayakan ‘yan ta’adda 30 a Mali, yayin farmaki kashi 2 da suka kaddamar kansu a ranakun Alhamis zuwa Juma’ar da suka gabata.

Wasu dakarun Faransa a Mali.
Wasu dakarun Faransa a Mali. Reuters/Benoit Tessier
Talla

Sojin na Faransa sun kaiwa ‘yan ta’addan farmakin ne a yankunan Gourma inda suka halaka 20 da kuma kone motocin yakinsu da dama, sai kuma yankin Liptako, inda mayaka masu biyayya ga IS ke da karfi, inda a nan kuma dakarun na Faransa suka halaka mayaka 10.

A watan Disambar da ya gabata ma, sojojin na Faransa sun halaka mayakan ‘yan ta’adda akalla 33 a kasar ta Mali, yayin farmakin da ta kaddamar kansu akan iyakar kasar da Mauritania.

Yanzu haka dai Faransa na da dakaru dubu 4 da 500 karkashin rundunar Barkhane a Mali, wadanda ke taimakawa dakarun majalisar dinkin duniya akalla dubu 13 dake kasar.

A baya bayan nan ne dai Ministar tsaron Faransa Florence Parley ta sanar da shirin tura karin sojin kasar 600 zuwa Mali domin murkushe hare-haren ta'addancin dake karuwa a yankin Sahel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.