Isa ga babban shafi

Amurka na horar da sojojin kasashen Afirka ta Yamma

Yanzu haka dai a yankin tsakiya maso yammacin kasar Mauritaniya karkashin jagorancin kasar Amurka kimanin dakaru dubu 1.600 na kasashen Afrika ta yamma na gudanar da atasayen sojan hadin guiwa na shekar shekara.

Sojojin Afirka na samun horo daga takwarorin su na Amurka a kasar Murtaniya
Sojojin Afirka na samun horo daga takwarorin su na Amurka a kasar Murtaniya US Army/Richard Bumgardner
Talla

Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da Washington ke nazarin rage sojojinta daga nahiyar, kuma yawaitar hare haren yan ta'adda dake salwantar da rayukan mutane a kasshen yankin Sahel.

Atasayen mai suna " Flintlock " ana gudanar da shi ne tun a 2005 karkashin jagorancin rundunar Amruka a nahiyar Afrika (Africom) domin karfafa sojojin kasashe aminanta dake yankin yammacin Afrika, wajen iya tunkarar yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda, tare da kare kan iyakokinsu domin tabbatar da tsaron lafiyar a'l'ummominsu", kamar yadda ofishin jakadancin Amruka a Mauritaniya ya sanar.

daga cikin kasashen Afrika da suka halarci atasayen na bana sun hada ne da jamhuriyar Bénin, Burkina Faso, Kamaru, Tchad, Cap-Vert, Côte d'Ivoire, Ghana, Guinée, Mali, Mauritaniya, Maroc, jamhuriyar Niger, Najeriya, Sénégal da kuma kasar Togo.

Bugu da kari atasayen ya samu halartar wasu kasashen Turai da suka hada da Holand, Norvège, Pologne, Portugal, l'Espagne da kuma Britaniya

An dai bude  wannan atasayen na 2020 ne a ranar Litanin a garin Atar dake tsakiyar kasar Mauritaniya, zai kuma kawo karshensa ne a ranar 28 ga watan nan na Fabrairu a biranen Nouakchott da Kaédi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.