An kammala yakin neman zaben shugaban kasa a Togo
A ranar Alhamis za a kawo karshen yakin neman zaben shugaban kasa wanda za a yi ranar Asabar mai zuwa a Togo.
Wallafawa ranar:
Shugaban hukumar zaben kasar Tchambakou Ayassor, ya ce tuni hukumarsa ta dauki matakan da suka dace don tabbatar da cewa an isar da kayan aiki a rumfunan zabe dubu 9 da 300 a sassan kasar.
Mutane 7 ne ciki har da shugaba mai ci Faure Gnasingbe za su tsaya a takara a zaben na ranar Asabar.
'Yan adawa na ci gaba da bayyana damuwa kan takarar neman wa'adi na 4 da Shugaban kasar Faure Gnasingbe da ya gaji mahaifinsa wanda ya yiwa kasar rikon kama karya tareda murkushe duk wani bore daga bangaren yan adawa ya yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu