Isa ga babban shafi
Najeriya-Sadarwa

Najeriya ta kare bukatar ciwo bashin dala miliyan 500 don inganta NTA

Ministan yada labaran Najeriya Lai Mohammed ya kare bukatar ciwo bashin Dala miliyan 500 domin bunkasa ayyukan tashar talabijin din kasa ta NTA domin ganin ta inganta ayyukan ta da kuma fafatawa da manyan kafofin yada labarai na duniya.

Ministan yada labaran Najeriya Lai Mohammed.
Ministan yada labaran Najeriya Lai Mohammed. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Yayin ganawa da manema labarai, Ministan ya ce za’ayi amfani da bashin wajen gudanar da ayyuka guda 3 da suka hada da sabunta kayan aikin da tashar ke da su domin ganin ta yi aiki kamar yadda tashar talabijin din CNN da ke Amurka ke yi.

Sauran ayyukan sun hada da gina tashar sadarwa mallakar gwamnati wadda za ta inganta watsa shirye shiryen kafofin yada labarai da kuma wata Cibiyar yada labarai da ake kira ‘Media City’ a Ikorodu da ke Lagos, wanda zai bada damar yin ayyuka daban daban da suka hada samar da kayayyakin aikin kafofin yada labarai da wurin horar da ma’aikata da gidan sinima irin na kasashen duniya da otel na zamani da wurin yawon bude ido.

Ministan ya ce daga cikin Dala miliyan 500 da za’a ciwo bashi, za’a mayar da daukacin tashoshin NTA a Jihohi 36 irin na zamani da ofisoshin ta na shiyYa guda 12 da kuma tashoshin al’umma 76 da kafar ke da su.

Yayin da wasu ke yabawa da wannan gagarumin aiki wanda suka ce zai samar da ayyukan yi da kuma inganta tashar wajen ganin ta biya bukatun masu hulda da ita, wasu na kokawa kan ciwo bashin ba tare da yiwa tashar NTA garambawul wajen daidaita ma’aikatan ta dan ganin sun dace da zamani da kuma bunkasa tashar wajen ganin ta inganta ayyukan ta da kuma tsayawa da kafafuwan ta ba.

Malam Muhammad Hashim Suleiman na sashen koyar da ayyukan jarida da ke Jami’ar Ahmadu Bello a Zaria ya bayyana cewar inganta tashar NTA na tattare da wasu kalubale daban daban da suka hada da mayar da tashar mai samar da kudaden kan ta, sauya yanayin shugabancin ta domin kauda ita daga tafarkin ma’aikatun gwamnati zuwa hanyar tafiyar da kasuwanci.

Suleiman ya kuma kara da bukatar sauya yadda ake zaburar da ma’aikatan tashar da kuma kyautatawa wadanda suka yi kwazo ko zarra wajen gudanar da aikin su da kuma hukunta wadanda suka saba ka’ida.

CNN ta 'yan kasuwa ce, inji malamin, kuma wadda aka shirya manufofin ta kamar yadda ake bukata kuma aka mayar da hankali akai domin ganin an cimma manufa, abinda ya baiwa tashar damar samun gagarumar nasara, sabanin yadda ake tafiyar da tashar NTA a Najeriya.

Masanin harkar sadarwa ya ce samarwa tashar NTA kudaden da ta ke bukata ba tare da an sake mata fasalin shugabanci da yadda ake gudanar da ita ba, ba zai sauya komai dangane da yadda take ayau ba.

Suleiman ya kawo misalai da dama da suka shafi wasu ma’aikatun gwamnati masu muhimmanci da aka warewa makudan kudade amma suka yi batar dabo ba tare da an aiwatar da manufar samar masu da kudaden ba, irin su kamfanin samar da karafar Ajaokuta da kamfanin mulmula karafan Katsina da aikin sauya kafofin yada labarai zuwa na zamani da Hukumar Sadarwar Najeriya keyi, wanda ayau ya kaiga dakatar da shugaban ta saboda zargin badakala da makudan kudaden da gwamnati ta ware a karkashin minista Lai Mohammed.

Yanzu dai haka bukatar ciwo wannan bashi na gaban Majalisar Dattawan Najeriya wadda ke da hurumin amincewa ko kuma watsi da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.