Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Riek Machar ya koma matsayinsa na matamakin shugaban kasa

An rantsar da shugaban ‘yan tawayen Sudan ta Kudu Riek Machar a matsayin mataimakin shugaban kasa yau Asabar, matakin da ya bashi damar komawa cikin gwamnatin shugaba Salva Kiir a karkashin shirin sasanta rikicin kasar da yaki ya daidai ta.

Shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar.
Shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar. REUTERS/Jok Solomun
Talla

Bayan rantsuwar Machar ya shaidawa mutanen kasar cewar a shirye suke suyi aiki tare domin kawo karshen ukubar da suke ciki.

Wannan shine karo na 3 da shugaba Kiir da mataimakin sa Machar za suyi kokarin dinke barakar dake tsakanin su domin kafa gwamnatin hadin kai da zata kawo karshen yakin basasar da yayi sanadiyar hallaka rayukan akalla mutane 380,000, yayin da sama da miliyan 4 suka tsere daga muhallan su.

A karkashin wannan shirin, bayan Machar akwai kuma Karin guraban mataimakin shugaban kasa guda 4 daga bangarorin sauran jam’iyyun adawar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.