Isa ga babban shafi
Cambodiya

An bude sauraren karar tsoffin shugabannin Cambodiya

Kotun da ke shari’a laifukan yaki a kasar Cambodiya, ta fara sauraron karar da ake wa uku daga cikin shugabanin Khmer Rouge, da ake zargin da kisan kiyashi a kasar tsakanin shekarar 1975-1979.Kotun da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, na zargin shugabanin Khmer Rouge da kashe mutane miliyan biyu.Cikin shugabannin da ake zargi sun hada da Nuon Chea, wanda ake ganin na hannun damar tsohon shugaba Pol Pot ne wanda ya mutu a shekarar 1998.Tsuffin shugabannin wadanda dukkaninsu sun haura shekaru 80 ana zarginsu ne da aikata laifukan yaki.Tun a shekarar 1990 ne gwamnatin Cambodia ta nemi Majalisar Dinkin Duniya kafa kotun sauraren karar kisan kiyashin da ya auku a cikin kasar.Sauran wadanda ake tuhuma sun hada da tsohon shugaban kasa Khieu Samphan da Ieng Sary wanda tsohon Ministan harakokin wajen kasar ne. 

Tsoffin shugabannin Khmers rouge da ake zargin aikata laifukan yaki a Cambodia
Tsoffin shugabannin Khmers rouge da ake zargin aikata laifukan yaki a Cambodia AFP / Tang Chhin Sothy
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.