rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Cambodia

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

‘Yan adawa a Cambodia sun nemi taimakon Majalisar dunkin Dunya akan zaben da aka yi.

media
Gangamin Siyasa a Cambodia

Madugun ‘yan adawan kasar Cambodia Sam Rainsy ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta shiga tsakani domin a raba rikicin siyasar kasar daya barke sakamakon zaben da aka gudanar a kasar.


A cewar Madugun ‘yan adawar yin hakan zai kare zabin da mutane suka yi a zaben kasar mai cike da rikici da rudani.

Kasar ta Cambodia dai ta shiga rudanin siyasa tun bayan jam’iyar Firaminista Hun Sen ta CPP ta yi ikrarin lashe zaben da aka yi a watan da ya gabata.

Sai dai jam’iyar adawa ta CNRP ta ce tana ja akan nasarar da abokiyar hamayyarta ke ikrarin samu.

Madugun ‘yan adawar Sam Rainsy ya kuma bayyana cewar gobe Talata ne zasu gudanar da babbar zanga-zangar nuna rashin amincewa da zaben a gaban Ofishin Majalisar dunkin Duniya .

Wannan kuwa, domin neman Majalisar ta dunkin Duniya data shiga tsakani, domin magance matsalolin da wannan zaben ke ciki da kuma kare nasarar da mtane suka samu.

Ya kuma fadi hakan ne a wurin babban taron gangamin da aka gudanar.

Jam’iyyar CPP dai ta bayyana cewar ita ke da Kujerun Majalisa 68 daga cikin 123 na karamar Majalisar kasar, a yayinda CNRP keda 55.