Sri Lanka
Sri Lanka ta saka ‘Yan tawayen Tamil Tigers a cikin ‘Yan ta’adda
Gwamnatin Sri Lanka ta sanya sunayen wasu kungiyoyi 15 na ‘yan kabilar Tamils, a matsayin kungiyoyin ta’adda, a wani yunkuri na dakile ayyukan ‘Yan kungiyar da gwamnatin ke zargin suna kokarin sake farfado da tsohuwar kungiyar Tamils Tigers da aka rusa a shekara ta 2009.
Wallafawa ranar:
Talla
Gwamnatin kasar ta yi zargin cewa akwai alaka ta kud-da-kud tsakanin wadannan kungiyoyi da ake kira LTTE da kuma tsohuwar kungiyar ‘yan tawayen, dalilin da ya sa ta haramta masu gudanar da ayyukansu a cikin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu