Mutane da dama sun mutu a wata girgizan kasa a Nepal
Mutane kusan 30 aka ruwaito sun mutu a wata girgizan kasa mai karfin maki 7.3 da ta sake shafar yankin gabacin kasar Nepal kusa da tsaunin Everest bayan sama da mutane 8,000 sun mutu a mummunar girgizan kasa da ta abkawa Nepal makwanni biyu da suka gabata.
Wallafawa ranar:
Mahukuntan kasar sun ce adadin mutane kusan 30 suka mutu yayin da sama da 1000 suka samu rauni sakamakon girgizan kasar da ta shafi gabacin kasar.
Masu aiko da rahotanni sun ce Girgizan kasar ta auku ne da musalin karfe 12:35 na rana a gabacin Kathmandu babban birnin kasar bayan girgizan kasa mai karfi maki 7.8 ta yi mummunan ta’adi a yammacin Nepal makwanni biyu da suka gabata.
Girigizan kasar ta shafi yankin India tare da rusa gidaje a yankin kabilar Tibet a China.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu