Isa ga babban shafi
Kuwait

Mutane 25 sun mutu a harin Masallacin Shi’a a Kuwait

Wani harin kunar bakin wake da aka kai Masallacin ‘Yan shia karon farko a birinin Kuwait ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 25 tare da raunata wasu sama da dari biyu. Kungiyar na ta IS da ke da’awar kafa daular Islama a gabas ta tsakiya ta dauki alhakin kai mummunan harin.

Mutane 25 sun mutu a harin Masallacin Shi’a a Kuwait
Mutane 25 sun mutu a harin Masallacin Shi’a a Kuwait REUTERS
Talla

Rahotanni sun ce an kai hari ne a masallacin Imam Sadiq da ke lardin gabashin birnin kasar a lokacin da mutane ke gab da fara Sallar Juma'a.

Ana dai ci gaba da samun karuwar adadin wadanda harin ya rutsa da su har yanzu kuma Karon farko ke nan da aka kai irin wannan harin a masallacin jumma’a na ‘yan Shia a Kuwait.

Kungiyar IS da ke da reshenta da Lardin Najd ta yi ikirarin kai wannan harin karkashin jagoranci wani shugabanta Abu Suleiman al-Muwahhid.

Tuni dai kasashen Turai suka fara allawadai da wannan harin, tare da alakawarin hadin kai domin daukar fansa akan ayyukan ta’adanci.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kalillan bayan, Kakakin Kungiyar IS Abu Muhammad al Adnani ya bukaci al’ummar Musulmi su kaddamar da Jihadi domin mutuwar shahada a cikin watan Azumin Ramadan mai alfarma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.