Isa ga babban shafi
Isra'ila-Gaza

Shekara guda da Yakin Gaza

Isra’ila da Falasdinawa sun cika shekara guda da yakin da suka gwabza a Gaza wanda ya yi sanadiyar kashe Falasdinawa 2,251 da suka hada da yara kanana 500, yayin da aka kashe Yahudawa 73 cikin su har da sojojin Isra’ila 67.

Isra'ila ta rusa gidajen Falasdinawa da dama a Gaza
Isra'ila ta rusa gidajen Falasdinawa da dama a Gaza RFI/Murielle Paradon
Talla

Wani rahotan Majalisar Dinkin Duniya da aka fitar a watan jiya akan yakin, ya zargi bangarorin biyu da aikata laifukan yaki, tare da sukar Isra’ila akan hare haren da ta kai a gine ginen Majalisar da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Yakin da aka kwashe kwanaki 50 anayi ya bar Falasdinawa sama da 100,000 ba tare da matsuguni ba.

Wannan shi ne yaki na uku cikin shekaru shida, kuma shi ne mafi muni daga cikin yake yaken da Isra’ila da Falasdinawa a Gaza.

Kungiyar Hamas da ke wanzar da iko a zirin Gaza ta bayyana gudanar da bikin juyayi a yau Laraba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.