Isa ga babban shafi
Isra'ila-Hamas

Kasar Isra'ila ta musanta tattaunawa da Hamas

Kasar Israila tayi watsi da duk wani rahoto dake nuna cewar tana tattaunawa da kungiyar Hamas domin amincewa da tsagaita bude wuta na tsawon lokaci.

Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu REUTERS/Ahikam Seri/Pool
Talla

Ofishin Firai Minista Benjamin Netanyahu ya ce babu wata ganawa da gwamnatin kasar ke yi da Hamas kai tsaye, ko kuma ta bayan fage, ko kuma ta hanyar sanya wata kasa ta tattauna da Hamas a madadinta.

Kafofin yada labaran kasahsen Larabawa da na Turkiya duk sun ruwaito cewar bangarorin biyu na tattaunawa a tsakanin su.

Kimanin mutane dubu 2 da 200 ne suka rasa rayukansu a rikicin da aka shafe tsawon kwanaki 50 ana yi tsakanin Falasdinawa da Yahudawa  a cikin  watannin Yuli da Agusta na shekarar bara, kuma dubban gidaje ne rikicin ya shafa a yankin Gaza.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.