Isa ga babban shafi
Japan

An bude wata cibiyar Nukiliya a kasar Japan

Wata cibiyar Nukiliyan kasar Japan ta fara aiki a karon farko cikin shekaru 2, bayan da aka rufe ta sakamakon matsalar da aka samu a cibiyar Fukushima cikin shekarar 2011.

Cibiyar Nukilya ta Sendai a kasar Japan
Cibiyar Nukilya ta Sendai a kasar Japan REUTERS/Kyodo
Talla

Kamfanin dake kula da cibiyar yace an bude ta ne, bayan da aka mata nazarin karshe a yau Alhamis da rana.

A karshen watan da ya gabata, cibiyar ta kai makurar wutar lantarkin da zata iya samarwa, kuma yanzu lardin Kyushu ne zai amfana da wutar da ake samarwa a cibiyar ta Sendai, mai nisan KM 1,000 daga birnin Tokyo.

Sai dai kuma a wannan ranar ce wata kungiyar dake adawa da amfani da sinadarin Nukiliya ta mika wa mahukuntan lardin Kagoshima inda cibiyar take, bukatar neman a rufe ta.

Cikin watan Augustan da ya gabata aka bude cibiyar mai shekaru 31, karkashin tsauraran matakan kariya, sakamakon kokarinda mahukuntar kasar keyi na samar da makamashi mai araha, duk kuwa da adawa da ake samu daga wasu ‘yan kasar.

Bude cibiyar na zuwa ne bayan girgizar kasar sakamakon ambaliyar ruwan tsunami ta janyo nutsewar na’ororin sanyaya cibiyar Nukiliya ta Fukushima a cikin shekarar 2011, lamarin daya tilastawa mahukuntan kasar rufe cibiyoyin Nukiliya guda 50, tare da jin ra’ayoyin jama’a kan amfani da makamashin na Nukiliya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.