Isa ga babban shafi
Yemen

An kammala musayar fursunoni a Yemen

Dakarun da ke goyon bayan gwamnatin Yemen da kuma ‘yan tawayen kasar sun kammala musayar daruruwan fursunoni a yau Alhamis.

Dakarun Yemen da ke goyon bayan gwamnatin kasar
Dakarun Yemen da ke goyon bayan gwamnatin kasar REUTERS/Stringer
Talla

Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da bangarorin biyu suka amince da yarjejeniyar tsagaita musayar wuta yayin da tattaunawar zaman lafiya a tsakaninsu da majalisar dinkin duniya ke jagoranta a Switzerland ta shiga rana ta uku.

Wani mamba a kwamitin kula da fursunoni a Yemen, Mokhtar al-Rabbash ya bayyana cewa sun yi nasarar kammala shirin musayar fursunonin, inda aka yi musayar 'yan tawayen Houthi 370 da dakarun da ke goyon bayan gwamnatin 285.

Rahotanni sun ce, an aiwatar da musayar ce a garin Yafaa da ke yankin kudancin lardin Lahj, kusa da kan iyakar lardin Bayda.

To sai dai Kungiyar agaji ta Red Cross da ke birnin Sanaa, wadda a baya a ka taba sanya ta cikin shirin musayar fursunonin, ta ce ba ta da masaniya game da wannan musayar.

Sama da mutane 5,800 ne rikicin Yemen ya yi sanadiyar mutuwarsu kuma akasarinsu fararan hula ne, yayin da kimanin 27,000 suka jikkata daga watan Maris zuwa yanzu kamar dai yadda majalisar ;dinkin duniya ta tabbatar.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.