Isa ga babban shafi
kuwait

Kotun Kuwait ta daure likita saboda azabtar da 'yar aiki

Kotun Kuwait ta yanke wa wata likita hukuncin zama gidan yari har na tsawon shekaru hudu sakamakon azabtar da ‘yar aikinta har ta kusan makancewa.

Wata kotu a Kuwait
Wata kotu a Kuwait AFP PHOTO / YASSER AL-ZAYYAT
Talla

Jaridar Al-Wataran ta Kuwait ta rawaito cewa , likitar na yawaita jibgan ‘yar aikin wadda ‘yar asalin kasar Madagascar ce har ta kai ga rasa idonta na bangaren hagu.

A farko dai wata karamar kotu ta wanke likitar mai shekaru 55 daga aikata laifi amma kotun daukaka kara ta yanke mata hukuncin daurin shekaru hudu bayan an shigar mata da kara kan batun.

Kazalika kotun ta ci tarar likitar Dalar Amurka 2,500, sannan ta umarce ta da ta biya ‘yar aikin Dala 16,500 kwatankwacin Naira miliyan 4 kudin Najeriya saboda lahanin da ta yi mata .

Rahotanni sun ce da yiwuwar kotun kolin kasar ta shiga cikin lamarin.

Kimanin ‘yan aiki a gidaje 600,000 ne ke zaune a Kuwait, akasarin su daga kasashen Asiya yayin da yawan ‘yan asalin kasar bai wuce miliyan 1.3 ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.