An ceto mutane 4 bayan kwanaki 36 a karkashin kasa a China
An yi nasarar ceto wasu mutane hudu mahaka ma’adinai a kasar China bayan sun shafe kwanaki 36 makale a karkashin a kasa, al-amarin da aka bayyana a matsayin abin al-ajabi.
Wallafawa ranar:
An shafe sa’oi biyu ana aikin ceto mutanen daga karkashin kasa mai zurfin sama da mita 200 kamar yadda kafar talabijin ta CCTV a China ta rawaito.
Mutanen dai na cikin mahaka ma'adinai 29 da kasa ta rubta da su a ranar 25 ga watan Disamabn bara, to sai dai ba a gamsu da aikin ceton ba, lura da cewa akwai sauran mutane 13 da har yanzu ba a ji duriyarsu ba kuma a jumulce mutane 15 kenan aka ceto yayin da aka tabbatar da mutuwar mutun guda.
An dai kwatanta aukuwar lamarin da irin wanda ya faru a shekara ta 2010 a kasar Chile, inda aka ceto mutane 33 bayan suma sun shafe kwanaki 69 makale a karkashin kasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu