rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Ecuador Italiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Girgizar kasa ta kashe mutane 272 a Ecuador

media
An tura jami'an tsaro wurin da girgizar kasar ta auku ®REUTERS/Guillermo Granja

Gwamnatin Ecuador ta tabbatar da mutuwar mutane akalla 272 yayin da sama da 1,500 suka samu raunuka sakamakon girgizar kasa mai karfin gaske da ta afka wa kasar.


Tuni dai aka tura jami’an tsaro dubu 10 da suka hada da ‘yan sandan dubu 3 da 500 zuwa wurin da ibtila’in ya faru kuma ana ci gaba da aikin ceto.

Hukumomin kasar sun bayyana cewa da yiwuwar adadin mutanen da suka rasa rayukansu ya karu, lura da cewa ana kan tattara bayanai game da lamarin.

Shugaban kasar Rafael Correa ya katse ziyararsa a Italiya saboda ibtila’in da ya afka wa al’ummarsa kuma tuni ya kafa dokar ta baci tare da fadin cewa za a fi mayar da hankali ne wajen ceton wadanda ake zaton suna da rai.

Girgizar kasar dai mai karfin maki 7.8, ta auku ne a yammancin ranar Asabar din da ta gabata kuma ita ce mafi muni da kasar ta fuskanta cikin tsawon shekaru da dama.