Isa ga babban shafi
Thailand

Thailand : Sojoji sun yi nasara a zaben raba gardama

Sakamakon farko na zaben raba gardama da aka gudanar a Thailand kan sabunta kundin tsarin mulki, ya nuna cewa Sojoji sun samu nasara, matakin da zai ba su damar ci gaba da iko a kasar.

Shugaban Sojin Thailand Prayuth Chan-ocha
Shugaban Sojin Thailand Prayuth Chan-ocha
Talla

Kwarya-kwaryan Sakamakon da hukumar zaben kasar ta fitar ya nuna sama da kashi 60 sun amince da sabon kundin tsarin mulkin na Sojoji.

Hukumomin kasar sun ce sama da kashi 55 ne na al’ummar kasar suka fito kada kuri’ar cikin mutanen kasar sama da miliyan 50.

Wannan ne dai karon farko da mutanen Thailand suka kada kuri’a a zabe tun lokacin da kwamdandan Sojojin kasar Prayut Chan O Cha ya hambarar da gwamnatin Yingluck Shinawatra a 2014.

Sojojin sun ce sabon kudin zai yi yaki ne da cin hanci tare da tabbatar da zaman lafiya a kasar.

Sai dai tun hawan Sojojin babu abin da ya canja a Thailand.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.