Isa ga babban shafi
Turkiya

Sojin Turkiya sun kori mayakan ISIL daga Jarabulus

Sojojin Turkiya da tankokin yaki tare da hadin gwiwar ‘yan tawayen Syria sun samu nasarar korar mayakan ISIL daga garin Jarabulus.

Hayaki na tashi daga birini Jarabulus yayinda Turkiya ke fafatwa da mayakan ISIL
Hayaki na tashi daga birini Jarabulus yayinda Turkiya ke fafatwa da mayakan ISIL Reuters/路透社
Talla

Wannan nasara ta zo ne bayan da gwamnatin Turkiya ta bada umurnin kaddamar da yaki ta sama da kasa kan mayakan ISIL kwanaki kadan bayan harin kunar bakin wake da wani karamin yaro ya kai a kasar wajen wani taron biki.

Garin Jarabulus da ke kan iyakar Turkiya da Syria, ya kasance karkashin ikon mayakan ISIL tsawon shekaru 2 kafin nasarar da sojin Turkiya suka samu a kansu.

A wani jawabi da shugaban Turkiya a gabatar a ranar Laraba, Recep rdogan ya ce yakin zai kuma maida hankali kan tarwatsa mayakan Kurdawa na YPG, wadanda ke samun goyon bayan Amurka kuma suke kokarin dannawa birnin na Jarabulus.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.