rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Uzbekhistan Rasha Kyrgyzstan Kazakhstan

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

A na shirin jana'izar Karimov a Uzbekistan

media
Marigayi shugaba Islam Karimov na Uzbekistan REUTERS/Maxim Shemetov

A yau Asabar ne za a yi jana’izar shugaban kasar Uzbekistan Islam Karimov wanda aka sanar da rasuwarsa a yammacin jiya jumma’a bayan ya yi fama da matsanancin rashin lafiya.


Za a gudanar da jana’izar ce a mahaifarsa da ke birnin Samarkand, kafin daga bisani al’ummar kasar su fara zaman makoki na tsawon kwanaki.

Ana saran shugabannin kasashen duniya za su halarci jana’izar da suka hada da shugaban Rasha, Vladmir Putin da kuma Firaministocin Kyrgyzstan da Belarus da Kazakhstan.

Kawo yanzu dai babu tsayayyen mutumin da ake ganin zai gaji Karimov a matsayin shigaban kasa.