rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Cambodia Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Cambodia za ta hallaka masu yajjin aiki

media
Firaministan Cambodian Hun Sen TANG CHHIN SOTHY / AFP

Firaministan Cambodia Hun Sen,  ya yi alkawarin hallaka 'yan adawar kasar da suka shiga wani yajin aikin gama-gari saboda yadda gwamnati ke karan-tsaye, abin da ya janyo suka daga kasashen duniya.
 


Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun zargi Firaministan da kama mutane da dama da ke sukar yadda yake tafiyar da mulki, cikinsu har da mataimakin shugaban 'yan adawar, Kem Sokha.

A makon jiya ne kasashe 36 cikin su har da Amurka suka sanya hannu kan wata takardar korafi kan yadda gwamnatin kasar ke kama-karya a kasar.