Isa ga babban shafi
Afghanistan

Jirgin soji ya fadi a Afghanistan

Mutane 8 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon hadarin da ya rutsa da jirgin soji mai saukar ungulu a yankin Baghlan, uku daga cikinsu sojoji ne yayin da sauran suka kasance ma’aikatan jirgin.

Sojin Afghanistan a birnin Kabul bayan kai wani harin bam.
Sojin Afghanistan a birnin Kabul bayan kai wani harin bam. © Reuters
Talla

Hukumomin Afghanistan sun ce injin din jirgin ne ya samu matsala al’amarin da ya haifar da hadarin.

Sai dai tuni Kungiyar Taliban ta sanar cewa, mayakanta ne suka kakkabo jirgin wato jim kadan da faduwar jirgin.

Wannan na zuwa ne a yayin da gwamnatin Afghanistan ke kokarin kakkabe mayakan Taliban daga yankin Kunduz bayan samamen da mayakan suka kai akan birnin a makon jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.