Isa ga babban shafi
Lebanon

Aoun ya zama shugaban Lebanon

An zabi Michel Aoun, a matsayin sabon shugaban Lebanon wanda ya kawo karshen shekaru biyu da aka shafe babu shugaban kasa bayan shugaba Michel Suleiman ya sauka.

Michel Aoun sabon shugaban Lebanon
Michel Aoun sabon shugaban Lebanon REUTERS/Mohamed Azakir
Talla

Michel Naim Aoun, tsohon Janar ne na Soja da Kungiyar Hezbollah ke marawa baya.

Aoun shi ne shugaba na 13 a Lebanon bayan shugaba Michel Suleiman ya sauka a lokacin da wa’adin mulkin shi ya kawo karshe a watan Mayun 2014.

A shekarar 1938 aka haifi Aoun a yankin Haret Hreik da ke cakude da kiristoci da ‘yan shi’a a Lebanon

A 1995 ya shiga aikin soja kuma yana cikin dakarun da suka yi yakin basasa a Lebanon, ya taba rike mukamin Firaminista, inda a lokacin ne ya yaki dakarun Syria a 1989, kafin su abkawa Beirut a 1990 har ya sa Aoun ya tsere zuwa Faransa.

Sai bayan ficewar dakarun ne na Syria Aoun ya dawo Lebanon kuma a lokacin ne ya kulla kawance da kungiyar Hezbollah duk da ya yi yaki da Hafez Al Assad mahaifin shugaban Syria na yanzu Bashar al Assad.

Aoun ya dade yana harin zama shugaban kasa, kuma a yanzu ya samu goyon bayan manyan masu hammaya da shi Samir Geagea shugaban kungiyar Mayaka Kiristoci da kuma tosohon Firaminista Saad Hariri da ake sa ran zai ba mukamin Firaminista.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.