Isa ga babban shafi
Colombia

Sabuwar yarjejeniya tsakanin gwamnati da 'yan tawayen FARC

Gwamnatin kasar Colombia da ‘yan tawayen kungiyar FARC sun sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya makonni shida da wargajewar yarjejeniyar farko da aka kulla bayan al’ummar kasar sun yi watsi da shirin a zaben raba gardama.

Shugaba Juan Manuel Santos da jagoran 'yan tawayen FARC Timochenko.
Shugaba Juan Manuel Santos da jagoran 'yan tawayen FARC Timochenko. Luis ACOSTA / AFP
Talla

Shekaru hudu bangarorin biyu suka kwashe suna tattaunawa da wakilan juna a kasar Cuba don gano hanyar kawo karshen yakin fiye da shekaru hamsin da aka gwabza da ya kuma yi sanadiyar rayukan mutane sama da dubu dari biyu baya ga mutane miliyan shida da suka rasa matsugunni.

Bayan sakamakon zaben raba gardamar Shugaban kasar Juan Manuel Santos ya sha alwashin sake koma teburin tattaunawa don warware rikicin, a baya ma dai shugaba Santos ya lashe kyautar yabo ta zaman lafiya bisa kokarinsa na kula yarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan tawayen Farc.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.