Hukuncin daurin rai da rai kan masu hannu a yunkurin juyin mulki
Masu shigar da kara a Turkiya sun bukaci hukuncin dauri na iyakacin rayuwa kan mutane akalla 50 da ake zargi da yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a watan Yulin da ya gabata.
Wallafawa ranar:
Ana zargin mutanen ne da hadin baki domin kashe shugaba Recep Tayip Erdogan a wani wurin hutawa inda shugaban ya ke tare da iyalansa a lokacin.
Daga wannan wurin shakatawa ne dai Shugaban ya bar wajen ba shiri zuwa birnin Santanbul inda ya ke cewa ya bar wurin ana saura mintoci 15 a kashe shi.
Tun bayan wannan yunkurin juyin mulkin shugaba Erdoghan ya sa ana tsare mutane fiye da dubu uku a gidan yarin kasar baya ga wasu da dama da aka sallama daga aiki bisa zargin hannu a juyin mulkin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu