Isa ga babban shafi
Philippines

Saudiya ta yankewa Iraniyawa hukuncin kisa

Wata kotu a kasar Saudiya ta yankewa wasu mutane 15 hukuncin kisa saboda samun su da laifin yi wa kasar Iran leken asiri.

Ministan harkokin wajen kasar Saudiya Saud al-Faisal
Ministan harkokin wajen kasar Saudiya Saud al-Faisal REUTERS/Faisal Al Nasser
Talla

Rahotanni sun ce akasarin wadanda aka yankewa hukuncin sun fito ne daga cikin mabiya Shi’a dake kasar.

An dai fara shari’ar ce a watan Fabarairu, wata guda bayan da Saudiya ta yanke huldar jakadanci da Iran saboda kona ofishin jakadancin ta da ke Tehran.

Masu gabatar da kara sun zargi mutanen da bayyanawa Iran bayanan asirin da suka shafi tsaro da kuma daukar masu basu bayanai daga cikin hukumomin gwamnati.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.