Isa ga babban shafi
Myanmar

Amnesty International ta fitar da sabon rahoto kan Myanmar

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International, ta ce matakan musgunawa da jami’an sojin Myanmar ke dauka kan Musulmi ‘yan kabilar Rohingya a kasar, babban laifi ne na take hakkin dan’adam.

Wasu 'yan kabilar Rohingya da ke gujewa cin zarafin sojin kasar Myanmar
Wasu 'yan kabilar Rohingya da ke gujewa cin zarafin sojin kasar Myanmar
Talla

Cikin sabon rahoton da ta fitar, kungiyar ta Amnesty, ta zargi sojin kasar Myanmar da yiwa fararen hula da suka fito daga kabilar Rohingya kisan gilla, yiwa matansu fyade, azabtarwa, da kuma sace musu dukiya.

Tun a watan Ocktoban da ya gabata, rahotannin cin zarafi da take hakkin dan adam suka fara bulla daga jihar Rakhine da ke kasar ta Myanmar, bayanda sojin kasar suka kaddamar da abinda suka kira yaki da masu neman tada kayar baya a jihar.

An dai kaddamar da matakin murkushe wadanda rundunar sojin kasar ke dauka a matsayin masu tada kayar baya ne daga kabilar Rohingya, bayan wani hari da suka kai kan wani ofishin ‘yan sanda a jihar Rakhine.

A watan Nuwamba da ya gabata, kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch, ta fidda hotunan da ke nuna yadda sojin Myanmar suka kone kauyuka da dama na Musulmi ‘yan kabilar Rohingya, bayaga kisan gillar da suka yiwa da dama.

Sai dai fa har yanzu, rundunar sojin Myanmar na cigaba da musanta take hakkin dan adam da ake zarginta da aikatawa, inda ta ce tana yaki ne kawai da ‘yan ta’adda.

A haliln da ake ciki dai manyan jagororin kudu maso gabashin nahiyar Asiya, sun fara taro a birnin Yangon na Myanmar somin tattaunawa kan yadda za’a kawo karshen, wannan tashin hankali.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.