Isa ga babban shafi
Afghanistan-UAE

An kashe jami'an diflomasiyar UAE a Afghanistan

Jami’an Diflomasiyyar Haddadiyar Daular Larabawa biyar na daga cikin mutane 50 da suka rasa rayukansu sakamakon harin bam da mayakan Taliban suka kai a jiya Talata a garin Kandahar na kasar Afghanistan.

Daya daga cikin wadanda suka raunana a harin na Taliban
Daya daga cikin wadanda suka raunana a harin na Taliban REUTERS/Mohammad Ismail TEMPLATE
Talla

An kai wannan harin ne a lokacin da tawagar ta jami’an diflomasiyar da ta kunshi jami’an agaji da kuma bunkasa ilimi ke ziyara a yankin na Kandahar, daya daga cikin yankunan da ‘yan Taliban ke da dimbin magoya baya a kasar.

Tuni dai gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku sakamakon wannan rashin.

Shugaban Daular, Sheik Khalifa bin Zayed ya bada umarnin sauke daukacin tutocin kasar zuwa tsaka-tsaki don karrama jami’an na diflomasiyar.
 

An kaddamar da hare-haren ne a birane uku na Afghanistan a jiya, abin da ya yi sanadiyar mutuwar jumullar mutane 50 tare da jikkata fiye da 100.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.