Isa ga babban shafi
Syria-Jordan

An kai harin bam kan sansanin 'yan gudun hijira na Rakban

Wani bam da aka boye cikin mota ya tarwatse a cikin sansanin ‘yan gudun hijira na Rakban da ke Syria wanda ke kusa da iyakar kasar da Jordan. 

sansanin yan gudun hijira na Rakban a Syria kusa da iyakar Jordan.
sansanin yan gudun hijira na Rakban a Syria kusa da iyakar Jordan.
Talla

Ko da yake ba bayyana adadadin wadanda suka rasa rayukansu ba, kungiyar kare hakkin dan’adam da ke sa’ido a Syria, da aka fi sani da Syrian Observatory a turance, da ke da cibiyarta a Birtaniya ta mutane da dama suka mutu yayinda wasu suka samu raunuka.

Sansanin ‘yan gudun hijirar na Rakban na dauke ne da fararen hula, da kuma mayakan ‘yan tawaye, da ke yakar kungiyar IS, da kuma gwamnatin Bashar al-Assad a lokaci guda.

Babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin kan sansanin da ke dauke da mutane 85,000.

Harin na zuwa yayinda ya rage kwana daya a fara tattaunawar sulhu tsakanin gwamnatin Syria da ‘yan tawayen kasar gobe Litinin a birnin Astana na kasar Kazakhstan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.