rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Korea ta Arewa Malaysia

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An kashe dan uwan shugaban Koriya ta Arewa a Malaysia

media
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un AFP

Wasu mata biyu Jami'an leken asiri da rahotanni suka tabbatar da ‘yan asalin kasar Koriya ta Arewa ne sun kashe dan uwan shugaban kasar Kim Jong-Un a Malaysia ta hanyar yi ma shi allura da sinadari mai guba.


‘Yan sandan Malaysia ne suka tabbatar da mutuwar Kim Chol a lokacin da ya ke kokarin zuwa Asibiti daga tashar jirgin sama a birnin Kuala Lumpur.

Amma rahotanni daga Koriya sun ce ya yi amfani da takardun jabu ne inda suka bayyana asalin sunansa a matsayin Kim Jong-Nam.

Majiyoyi sun ce, a halin yanzu ana gudanar da bincike kan gawar Kim Jong-Nam mai shekaru 45 wanda mahaifinsu guda da shugaban Koriya na yanzu Kim Jong-Un wato tsohon shugaban Korea ta Arewa marigayi Kim Jong-il.