Isa ga babban shafi
Syria

Sabani ya sa 'Yan tawayen Syria na kashe junansu

Wani rikici da ya barke tsakanin kungiyoyi biyu na ‘yan tawayen Syria da ke dasawa da juna, ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 70 a cikin sa’oi 24.

'Yan tawayen Syria da ke fada da dakarun gwamnatin Assad
'Yan tawayen Syria da ke fada da dakarun gwamnatin Assad REUTERS/Khalil Ashawi
Talla

Kungiyoyin Fateh al Sham da kuma Jund al Aqsa da ke lardin Idlib sn samu Baraka ne a tsakaninsu, inda a can baya suka hada kai don yaki da dakarun gwamnatin shugaba Bashar Assad.

Kungiyar da ke sa ido kan Syria mai cibiya a Birtaniya ta ce, rikicin ya barke ne bayan Jund al Aqsa ta kai harin bam a shalkwatan Fateh al Sham, in da ta kashe mambobinta 9.

Wannan na zuwa a yayin da ake kokarin shawo kan rikicin Syria a Kazakstan tsakanin bangaorrin ‘Yan tawayen da suka rarrabu da kuma bangaren gwamnatin Assad.

A gobe Laraba ake sa ran gudanar da tattaunatawar a birnin Astana tsakanin wakilan ‘Yan tawaye da gwamnati karkashin jagorancin Iran da Rasha da kuma Turkiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.