Isa ga babban shafi
Colombia

Tsugune ba ta kare ba a kasar Colombia

A Colombia mutanen da ke zaune akan iyakar kasar da Venezuela ne ke tserewa suna barin gidajensu sanadiyar ayyukan wasu kungiyoyin ‘yan tawaye da suka bijiro bayan da ‘yan tawayen FARC suka rungumi shirin zaman lafiya a yarjejeniyar da aka cimma a tsakaninsu da gwamnatin shugaba Juan Manuel Santos.

Iyalai da dama ne suka kauracewa gidajensu a Colombia.
Iyalai da dama ne suka kauracewa gidajensu a Colombia. wikimédia
Talla

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, inda ta bayyana fargabarta kan makomar mutanen da yanzu ke tserewa daga kasar don rikicin ‘yan tawayen.

Da dama sun tsere daga gidajensu zuwa Venezuela Makwabciyar kasar yayin da sauran suka nemi mafaka a sansanonin ‘yan gudun hijra.

Shekaru fiye da hamsin aka kwashe ana fama da rikicin kungiyoyin ‘yan tawaye na FARC a Colombia al’amarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da dubu dari biyu.

Shugaba Juan Manuel Santos ya ci gaba da kokarin ganin an mutunta yarjejeniyar da gwamnatinsa da shugabanin kungiyoyin ‘yan tawayen Farc suka cimma don tabbatar da zaman lafiya dawamammiya a kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.